Rundunar sojin Najeriya ta yi alƙawarin kuɓutar da fiye da ɗalibai 200 da ƴanbindiga suka sace

0 221

Rundunar sojin Najeriya ta yi alƙawarin kuɓutar da fiye da ɗalibai 200 da ƴanbindiga suka sace a baya-bayan nan a jihar Kaduna.

Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja game da ayyukan rundunar sojin a makonni biyu da suka gabata, Daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ya ce sojojin a shirye suke su ceto ɗaliban ba tare da an rasa rai ba.

Ya kuma ɗora laifin sace ƴangudun hijira a kwanakin da suka gabata daga Gamboru-Ngala a jihar Borno kan rashin mutunta umarni inda suka fita daga sansanin domin neman itacen girki ba tare da sanar da jami’ai ba.

Tun dai bayan sace ɗaliban ne, shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su gano ƴanbindigar tare da kuɓutar da ɗaliban inda ya nanata cewa gwamnati ba za ta biya kuɗin fansa ba. Bayan taron majalisar zartaswa na ranar Laraba ministan yaɗa labaran ƙasar Muhammad Idris ya bayyana hakan inda ya shaida wa ƴanjarida cewa shugaba Tinubu ya nanata umarnin tabbatar da kuɓuto ɗaliban da mayar da su ga iyalansu lami lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: