Shugaban rundunar sojoji ta kasa Laftanal Kanal Taoreed Lagbaja yace dokar zama a gida a yankin kudu maso gabashin kasar nan yazo karshe.
Ya bayyana haka ne jiya yayin taron shugabannin rundunar na karshen wannan shekarar.
A cewar sa,yace an kawo karshen dokar ne biyo bayan kokarin da jami’an tsaron kasar nan ke yi na magance matsalar tsaro a kasar nan.
Shugaban rundunar sojjin yace ayyukan Boko Haram da sauran yan ta’adda sun ragu sosai
Ya kara da cewa mazauna yankunan sun koma harkokin kasuwancin su. Kanal Taoreed Lagbaja yace rundunar sojin Najeriya ta samar da sabbin jami’ai na musamman domin yaki da matsalolin tsaro a Fadin kasar nan.