Rundunar sojin Najeriya ta ce ta mika tubabbun ‘yan Boko Haram sama da 565

0 184

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta mika tubabbun ‘yan Boko Haram sama da 565 ga Gwamnatin Jihar Borno.

Birgediya Janar Benard Onyeuko wanda shi ne mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar ne ya sanar da hakan yau a Abuja, lokacin da yake tattaunawa da manema labarai, in da ya ce tuni aka mika wa gwamnatin mutanen domin ci gaba da kula da su bayan dogon bincike.

Janar Benard yace cikin wadanda aka mika akwai wasu manyan kwamandoji uku, da barayin shanu biyar da kuma iyalansu.

Ya kara da cewa daga ranar 12 ga watan Agusta zuwa 1 ga watan Satumba sama da ‘yan tada kayar baya dubu 5 da 890 ne suka mika wuya ga dakarun rundunar HADIN KAI a arewa maso gabashin kasarnan.

Ya kara da cewa an kwace kananan makamai da suka kai 52 da harsasai kimanin dubu 1 da 977, ciki har da bindiga kirar AK-47 da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: