Rundunar Sojin Najeriya ta ce kimanin mayakan Boko Haram 219 ne suka mika wuya
Rundunar Sojin Najeriya ta ce kimanin Mayakan Boko Haram 219 ne suka mika wuya ga rundunar wanda take aiki a yankin Arewa Maso Gabashin kasar nan.
Daraktan Yada Labarai na Rundunar Brigadier General Onyema Nwachukwu, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, inda ya ce lamarin ya faru a jihar Borno cikin karshen makon daya gabata.
Brigadier General Onyema ya ce Mayakan Boko Haram sun mika kansu ne ga rundunar da take yaki a Bama a ranakun 2 da 4 ga wata.
A cewarsa, kawo yanzu Mayakan ISWAP basu karyata labarin da ke cewa ana rage musu karfi ba.
Brigadier General Nwachukwu, ya ce yan Boko Haram suna cikin fargaba ne saboda hare-haren da Sojoji suke kai musu a maboyarsu ta Tumbus da Sambisa.
Kazalika, ya ce rundunar tana cigaba da kaiwa hare-hare kan yan Boko haram da yan bindiga da kuma masu Garkuwa da mutane domin kudin fansa.