Rundunar sojin saman ta Operation Hadirin Daji, ta yi wa ‘yan bindiga kwanton bauna a lokacinda suke shirin kai hare-haren ta’addanci a wasu yankuna a jihar Zamfara.
Manema labarai sun tattaro cewa ‘yan bindigar da suke neman mafaka sun gamu da ajalin su ne a wani samame da sojojin suka kai a kauyen Makaruwa.
Yan bindigar sunyi shirin kai Hare-haren ramuwar gayya ne kafin rundunar Operation Hadirin Daji ta dakile harin inda sojojin suka far musu tare da yi musu kwantan bauna.
A cewar mai magana da yawun rundunar ‘Operation Haderin Daji’, Laftanar Sulieman Omole, yace rundunar ta jaddada ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso yammacin kasar nan, wanda ke nuni da yakar ‘yan ta’adda da ke barazana ga zaman lafiyar yankin.