Rikicin Makiyaya: Gwamnatin Ekiti ta bai wa makiyaya wa’adi su yi rijista ko su bar jihar

0 218

Gwamnatin jihar Ekiti ta bai wa manoma da makiyaya wa’adin makwanni biyu, su yi rijista da gwamnatin jihar ko kuma su fice daga jihar baki daya.

Tuni wa’adin ya fara aiki tun ranar Lahadi, 22 ga watan Maris.

Cikin wata sanarwar kwamishinan aikin gona da wadatar abinci na jihar Dakta Olabode Adetoyi, ya bayyana cewa gwamnati ta lura cewa rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya na haifar da haɗari ga lafiyar mutane da kuma ƙoƙarin wadata jihar da abinci, don haka ɗaukar wannan mataki ya zama wajibi ga gwamnati, don dakile matsalar.

A watan Fabrairun da ya wuce ne jihar ta gudanar da rajista ta tsawon makwanni biyu, ga manoma da makiyaya, sai dai hukumomi sun ce ba dukkaninsu ne suka yi ba.

Mashawarci na musamman ga Gwamna Kayode Fayemi kan lamuran tsaro kuma shugaban kwamitin sasanta makiyaya da manoma a jihar Birgediya-Janar Ebenezer Ogundana mai ritaya., ya yi gargadi a cikin sanarwar, yana cewa ”Za a kori duk wanda ya ƙi yin wannan rajista daga jihar”.

Yadda jihohin kudu suka haɗe kai kan wannan batu

Gwamnonin Kudu Maso Gabashin Najeriya
Bayanan hoto,Gwamnonin Kudu Maso Gabashin Najeriya

Tuni dama kungiyar gwamnonin yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya sun haramta yin kiwo barkatai, kamar yadda shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin David Umahi ya ce.

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ce: “Muna cikin wani mummunan lokaci, idan babu kishin ƙasarmu Najeriya a ranmu, zai yi wahala a samu zaman lafiya.

“Ya kamata shugabanni da masu ruwa da tsaki na wannan yankin su magantu su kuma daina sanya siyasa a cikin tsaron yankin da na ƙasar baki ɗaya.

“Gwamnonin Kudu Maso Gabas sun yi kira ga shugabanninmu da su yi magana a kan tsaron yankin da kuma haɗin kan Najeriya. Na karanta a jarida inda wani ya ce ya bai wa gwamnonin Kudu Maso Gabas kwana bakwai da su haramta kiwon barkatai.

“Gwamnonin Kudu Maso Gabas sun haramta kiwo barkatai da zirga-zirgar makiyaya da shanunsu da ƙafa a yankin, za mu kula da kanmu sosai, abin da muka tattauna da makiyayan abu ne da yake kan tsari tsawon lokaci.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: