Rikici ya barke a jihohi da dama kan ‘yancin cin gashin kai na kananan hukumomi

0 152

Bayan hukuncin Kotun Koli da ya ba wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu, rikici ya barke a jihohi da dama saboda fassarar hukuncin ta hanyoyi daban-daban.

Kotun ta yanke hukunci ne a ranar 11 ga watan Yulin bara, inda ta tabbatar da cewa jihohi ba su da ikon rushe zababbun shugabannin kananan hukumomi.

Sai dai, bayan watanni takwas, har yanzu aiwatar da wannan hukunci yana fuskantar cikas sakamakon matsalolin siyasa.

A wasu jihohin, kamar Osun da Rivers, an samu matsaloli da rikice-rikicen siyasa dangane da yadda za a aiwatar da hukuncin, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da rikicin jam’iyyun siyasa. 

Leave a Reply