Ribar biliyan 141 kamfanin mai na NNPC ya samu a watan Yunin wannan shekarar

0 165

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya sanar da samun ribar naira biliyan 141.96 a watan Yunin 2021 idan aka kwatanta da asarar naira biliyan 37.46 da ya yi a watan Mayu na shekarar.

Sanarwar da kamfanin ya fitar ranar Lahadi ta bakin shugaban sashen hulɗa da jama’a Garba Muhammad ta ce bayanan hakan na ƙunshe ne cikin rahoton wata-wata na Yuni.

Ana gane riba ko faɗuwa ne bayan an ware kuɗaɗen gudanarwar kamfanin daga cinikin da aka yi na lokacin da ake magana.

Rahoton ya bayyana cewa a Yunin 2021, kuɗin shigar da NNPC ya samu ya ragu da kashi 9.07 cikin 100 zuwa biliyan 89.27 daga 894.64 idan aka kwatanta da watan Mayu. Kazalika, ya ce kuɗin gudanarwa ma ya ragu zuwa biliyan 299.44 daga 721.93 a Mayun.

Sanarwar ta ƙara da cewa an samu ribar ce sakamakon ƙaruwa da aka samu ta yawan ɗanyen mai da kuma iskar gas da NNPC ke fitarwa.

Asalin rahoton;

https://www.bbc.com/hausa/live/labarai-59634803

Leave a Reply

%d bloggers like this: