Rayuwar ‘yan Najeriya ta shiga cikin matsanancin halin kunci karkashin gwamnatin Tinubu – NLC/TUC

0 216

A yayin da Najeriya ta shiga sahun sauran kasashen duniya wajen murnar zagayowar ranar ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC, da Kungiyar ‘Yankasuwa, TUC, sun bayyana rayuwar ‘yan Najeriya a matsayin wadda ta shiga cikin matsanancin halin kunci karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

A sanarwar da kungiyoyin suka fitar, Shugaban Sashin Yada Labarai da Hulda da Jama’a na NLC, Benson Upah da Shugaban Kungiyar ‘Yankasuwa, Festus Osifo sun alakanta tsananin matsin tattalin arazikin da ‘yan Najeriya ke ciki da tsananin hauhawar farashi da matsalolin canjin kudaden waje da kuma matsalar makamashi.

Sun bayyana cewar wadannan abubuwa sun tsananta matuka a gwamnatin Tinubu saboda cire tallafin mai da sakin naira ta nemawa kanta kasuwa da kuma karin kudin lantarki da gwamnatin ta yi.

Domin magance wannan yanayi da ake ciki, Ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce suna fafutuka don ganin hukumomi sun amince da sabon mafi ƙarancin albashi, wanda zai dace da halin matsi da tsadar rayuwa da kuma tsananin hauhawar farashin da ake ciki.

Sun dai gabatar da buƙatar ganin mafi ƙarancin albashin ya kai sama da naira dubu ɗari shida, abun da wasu ke ganin zai wahala gwamnatin ta amince da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: