Sufeto Janar na Yansanda, Mohammed Adamu, ya dakatar da bukatar cancanta domin wadanda ke neman shiga aikin dansanda a matsayin kurata.
Mohammed Adamu a wani umarni da ya bayar, yace babu wadanda za a hana dama a wajen daukar aikin, bisa la’akari da yanayin halittarsa ko shekarunsa ko matakin karatunsa.
- An tara kudaden shiga sama da ₦15,000,000 a karamar hukumar Kafin Hausa
- Jirgi mai saukar Ungulu na farko da aka haɗa a Najeriya ya kusa kammaluwa
- NAFDAC ta ce ta karbe wasu magungunan da USAID take bayarwa a matsayin tallafi
- Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukan su a jihar Borno
- A yau Alhamis ne ake sa ran za a ci gaba da sauraron ra’ayin jama’a kan batun ƙudurin haraji da shugaban Najeriya ya aike wa majalisun dokokin ƙasar
Hukumar a halin yanzu tana aikin daukar kuratan yansanda dubu goma domin magance karancin yansanda, kuma tuni aka fara aikin tantance masu neman aikin daga jiya Litinin zuwa ranar goma sha shida ga watan gobe na Satumba.
Kamar yadda yazo a wata sanarwa da kakakin hukumar dansanda, Frank Mba, ya fitar, ana sa ran masu neman shiga aikin suzo da number shaidar zama dan kasa da takardun karatu na ainihi da kwafi bibiyu, da takardar shaidar zama dan karamar hukuma da ta haihuwa, wadanda aka shirya cikin fararen files guda biyu, tare da kananan hotuna na fasfo.