A wani makamancin wannan, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Labour Peter Obi a shekarar 2023, yayi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da isassun kudi ga dakarun sojoji da hukumomin tsaron kasar nan domin karfafa ayyukan su a fadin kasar nan, biyo bayan harin jirgin sama maras matuki da aka kai bisa kuskure Kauyen Tudun Biri dake Karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
Mista Obi yayi wannan kira ne yayinda ya ziyarci wadanda harin ya shafa a asibitin koyarwa na Barau Dikko a jiya.
Peter Obi, Ya koka dangane da yadda aka samu irin wannan hari bisa kuskure sau 16 tare da sanadiyyar rayuka sama da 500 a kasar nan,wanda a cewar sa babu abinda gwamnatin tarayya tayi domin kare afkuwar irin haka nan gaba.
Tsohon gwamnan Jihar ta Anambara, ya bukaci gwamnatin tarayya ta taimakawa dakarun sojojin kasar nan domin tabbatar da cewa irin haka bai sake faruwa ba nan gaba.
Ya bayyana cewa samar da isassun kudi ga dakarun sojojin kasar nan da sauran hukumomin tsaro zai taimakawa wajen magance matsalar tsaro a fadin kasar nan. Peter Obi, ya kuma goyi bayan kiraye-kirayen da ake na gudanar da bincike kan wannan harin, da samar da gidauniyar tallafawa wadanda harin ya shafa musamman ma wadanda suka zama marayuwa sanadiyyar harin.