Peter Obi ya ziyarci gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed

0 31

Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya kai ziyarar tuntuɓa ga gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed.

Cikin wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a lokacin ziyarar sun tattauna batutuwa da dama da suka danganci haɗin kai da yaƙi da rarrabuwar kawuna.

Gwamnan ya ce tattaunawar tasu ta ƙara ƙarfafa kishin ƙasa domin shimfaɗa tafiyar da ya ce ”za ta kyautata makomar ƙasar”.

Rahotonni sun ce ƴansiyasar biyu sun yi ganawar sirri a tsakaninsu, kafin daga baya a bar ƴanjarida su shiga.

Peter Obi ya bayyana cewa ya kai ziyara zuwa Bauchi ne domin jaje da ta’aziyyar mace-macen da aka yi a jihar, tare da tattauna a batutuwan da suka shafi makomar Najeriya da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a fagen siyasar ƙasar.

Leave a Reply