Oluremi Tinubu jiya ta bada gudunmawar Naira Milyan 500 ga iyalai 500 a jihar Filato

0 263

Matar shugaban kasa Oluremi Tinubu, a jiya ta bada gudunmawar Naira Milyan 500 ga iyalai 500 a jihar Filato biyo bayan tashin hankali da aka samu a jihar.

Wadanda suka amfana da wannan tallafin an tsakulo su ne daga kananan hukumomi 6 arewa ta tsakiyar Jihar.

Oluremi Tinubu, taje jos a jiya fadar gwamnatin jihar, domin jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su,tare da karfafa musu gwiwar kada su karaya da gwamnatin mijin ta shugaba Tinubu a kokarin da yake na maida zaman lafiya yankunan.

Matar shugaban kasar, ta kuma bayyana damuwar ta dangane da tashin hankalin da ake samu a jihar,musamman a yankin Mangu,inda ta nuna matukar damuwar ta yadda aka rasa rayuka da lalata muhallai a yankin.

Oluremi Tinubu,  ta bayyana cewa ta bada wannan talafi domin taimakawa iyalan wadanda rikicin ya shafa da abubuwan bukatu na yau da kullum.

Anasa jawabin, gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang  ya yabawa matar shugaban kasa dangane da wannan tallafi.

Kazalika, ya bayyana matar shugaban kasar a matsayin mace mai Jinkai da tausayin al’umma.

Gwamnan jihar ya kuma bukaci wadanda suka ci gajiyar wannan shiri da kada suyi son kai yayin raba kayan tallafin ga magidanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: