Ofishin NOA ya gudanar da taron fadakarwa kan Korona a Malam-Dori

0 219

Ofishin hukumar wayar da kan jama`a ta kasa a jihar Jigawa ta gudanar da taron gangami a karamar hukumar Malam-Madori domin fadakar da al`umma illolin da cutar Korona virus ta haifar a fannonin tsaro da zamantakewa.

A jawabin da ya gabatar Daraktan hukumar na jiha, Malam Shu`aibu Karamba Haruna yayi dogon bayani akan matakan da ya kamata a dauka domin kare yaduwar cutar Covid-19.

Haka kuma ya bukaci jama`a su tabbatar suna bin dukkanin ka`idojin da hukumomin lafiya suka tanada domin kare yaduwar cutar.

A lokacin gangamin wani jami`in hukumar wayar da kan jama`a ta kasa, Malam Tijjani ya gabatar da makala mai taken tasirin cutar Covid-19 akan tattalin arziki da karuwar aikata laifuka da kuma rigingimu tsakanin Fulani da manoma.

A nasa jawabin shugaban karamar hukumar Malam-Madori wanda ya sami wakilcin Daraktan tsare-tsare na yankin, Malam Lawan Bawa ya jaddada kudurin karamar hukumar na hada kai da hukumar domin cimma biyan bukata.

Mahalarta taron sun hadar da yan`kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyar Miyetti Allah da jami`an hukumar kiyaye haddura ta kada limamai da masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: