Ofishin INEC ya ƙone ƙurmus a jihar Sakkwato

0 100

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda  gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki.

Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa.

A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula da ofishin jihar, Hauwa Aliyu Kangiwa ta ruwaito.

Ya ce gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar Talata 11 ga watan Fabrairun 2025.

Leave a Reply