Nuhu Ribadu ya yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi na dakile barazanar tsaro

0 59

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yabawa rundunar sojojin, hukumar DSS, jami’an ‘yansandan da sauran jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi na dakile barazanar tsaro.

Ribadu ya kuma ce sanya ido tare da hadin kan ‘yan kasa ya taimaka wajen yaki da ta’addanci, da sauran matsalolin tsaro.

Ribadu ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Laraba, a cikin sakonsa na sabuwar shekara da ya gabatar ta hannun kodinetan hukumar yaki da ta’addanci ta kasa (NCTC), Manjo janar, Adamu Laka.

Ya yi nuni da cewa, nasarorin da aka samu a kokarin inganta tsaron kasar, sun samo asali ne daga hadin kan ‘yan kasar, da sadaukar da kai na jami’an soji, da sauran jami’an tsaro da kuma na jami’an leken asiri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: