Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya kawo ziyarar ta’aziyya ga Gwamna Umar Namadi na Jigawa a gidan gwamnati da ke Dutse, inda ya yi ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar gwamnan, Hajiya Maryam Namadi da dansa Abdulwahab Namadi.
Ribadu ya ce ya zo da kansa domin isar da ta’aziyyarsa bisa rashin damar yin hakan tun da farko, inda ya roƙi Allah ya ji ƙan mamatan.
A jawabinsa, Gwamna Namadi ya nuna godiya bisa wannan ziyara da ya ce ta nuna zumunci da mutunta juna da ke tsakaninsu.
Ana ganin dai, wannan ziyara ta kara jaddada ɗorewar zumunci da haɗin kai tsakanin waɗannan manyan shugabanni biyu a matakin ƙasa.