Nuhu Ribadu ya gana da gwamnoni 5 na jihohin kudu maso gabas jiya a Abuja

0 308

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya gana da gwamnoni 5 jihohin Kudu maso Gabas a Abuja jiya.

Duk da cewa ba a bayyana ajandar taron na sirri ga manema labarai ba, amma bata rasa nasaba da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a jihohin Anambra, Enugu, Abia, Imo da Ebonyi.

A ranar Larabar da ta gabata ne Majalisar Dattawa ta yi Allah-wadai da zaman da aka yi a ranar Litinin yankin Kudu maso Gabas tare da neman Gwamnatin Tarayya da ta hada kai da Gwamnatin kasar Finland tare da mika wani mai fafutukar kafa kasar Biafra, Simon Ekpa, domin gurfanar da shi gaban kuliya. Majalisar dattawan ta kuma yi watsi da shawarar a saki shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, inda ta ce yanzu maganar sakin sa na kan kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: