NOA ta fara wayar da kan al’ummar jihar Jigawa game da illolin cutar kwalara

0 176

Hukumar wayar da kan Al’umma NOA anan jihar Jigawa, tafara gangamin wayar da kan al’umma akan yanda zasu kare kansu daga kamuwa da cutar Kwalera wato amai da gudawa, a kananan hukumomi 27 dake fadin jihar nan.

Daraktan hukumar na jihar Jigawa, Shuaibu Karamba ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Dutse, inda ya tabbatar da cewa tini suka tura jami’ansu zuwa kananan hukumomi 27 wadanda zasu na wayar da kan al’umma domin dakile bazuwar cutar amai da gudawa.

Ya kara da cewa yanada kyau al’umma su kasance masu tsaftace muhallansu, da kuma jikin su a kowanne lokaci, harma da abincin da suke amfani da shi a kullum.

Darkatan ya kara da cewa wannan lokaci ne na gudanar gangamin yaki da wannan cutar da kuma gangamin wayar da kan al’umma akan bahaya a bainar jama’a.

kuma ya yabawa ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa da sauran masu ruwa da tsaki a fanni lafiya wajan kokarin yaki da wannan cutar, tare da bukatar al’umma su gaggauta kai rahoton wanda aka samu yanada kwalera ga bangaren bada agajin gaggawa na kananan hukumomi 27.

Leave a Reply

%d bloggers like this: