NNPC zai sayar da hannayen jarinsa a karon farko ga jama’a

Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) zai sayar da hannayen jarinsa a karon farko ga jama’a a cikin shekaru uku, wanda hanya ce ta tara kudaden shigar da ake bukata.
Shugaban kamfanin, Mele Kyari, ya fadawa kamfanin jaridar Bloomberg a cikin tattaunawar bidiyo yau cewa sayar da hannun jarin kamfanin a karon farko zai taimaka wa Najeriya ta ci gaba da kasancewar tare da kasashe masu arziki man fetur a duniya.
Kamfanin na NNPC a makon da ya gabata ya sanar da samun ribar Naira biliyan 287 a shekarar 2020, wanda shi ne na farko tun lokacin da aka kafa shi a shekarun 1970.
Najeriya ce kasa mafi yawan arzikin man fetur a nahiyar Afirka.
Amma arzikin baya nunawa akan rayuwar jama’ar kasarnan da yawansu ya kai sama da miliyan 200, inda mutane ke fama da matsanancin rashin aikin yi da bakin talauci.