NLC ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta jingine shirinta na yin ƙarin kuɗin wutar lantarki

0 602

Ƙungiyar Kwadago ta kasa NLC ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta jingine shirinta na yin ƙarin kuɗin wutar lantarki da kashi 40 cikin 100 a wata mai zuwa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Joe Ajaero ya fitar, wanda ya ce matakin zai ƙara wa ‘yan ƙasar musamman talakawa wahalhalu da matsin tattalin arziki.

Kafin hakan dai kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasa NERC na shirin ƙara kuɗin wutar daga ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa.

A wani mataki na janye tallafin da gwamnatin ƙasar ke biya kan kudin wutar lantarkin.

‘Yan ƙasar da dama sun bayyana kaɗuwarsu kan matakin ƙarin kuɗin wutar lantarkin, suna masu fargabar cewar zai haifar musu da ƙarin matsin tatalin arziki. A watan da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da matakin janye tallafin man fetur, lamarin da ya haddasa ƙaruwar farashin man fetur da na kayan abinci a faɗin ƙasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: