NLC na shirin tattaunawa da shugaba Bola Tinubu kan batun tsawaita shekarun ritaya

0 324

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC na shirin tattaunawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan batun tsawaita shekarun ritayar ma’aikatan zuwa shekaru 65.

Shugaban kungiyar NLC na kasa, Joe Ajaero, ya shaidawa manema labarai a jiya cewa, kungiyyar kwadago ba za ta ja da baya ba, ga manufar tsawaita shekarun da aka fara a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Idan zamu iya tunawa dai Kamfanin Dillancin Labaran na Kasa NAN ya ruwaito cewa kungiyar, a yayin bikin ranar ma’aikata a watan Mayun 2023 ta roki tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kara wa ma’aikatan gwamnati shekarun ritaya.

Sai dai kuma tsohon Karamin Ministan Kwadago na wancan lokacinFestus Keyamo ya shaida wa manema labarai cewa gwamantin shugaban kasa Muhammadu Buhari baza ta iya aiwatar da hakan ba.

Yanzu haka dai malaman makaranta dake karkashin ma’aikatun gwamnati a kowane mataki,su zasu fara amfana da shekaru 65 a matsayin shekarun yin rityar aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: