Kungiyar kwadago ta NLC ta yi barazanar tsayar duk wata hada-hadar tattalin arziki, muddin gwamnatin tarayya ta ki janye karin kudin man fetur da na wuta, cikin kwanaki goma sha hudu.
Shugaban kungiyar na kasa, Ayuba Wabba, ya sanar da haka a karshen zaman kwamitin aikin kungiyar na kasa, wanda aka gudanar jiya a Abuja.
- Matsalar wuta na ƙara ƙamari a jihohin Kano da makwabta
- Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 5 a Jihar Gombe
- An ƙaddamar da shirin rigakafin cutar Polio a yankin tafkin Chadi
- Nan da wata 6 yankin Arewacin Najeriya zai fitar da matsayarsa kan zaben 2027 – Hakeem Baba Ahmad
- An soki yadda aka kafa Kwamatin Kidaya a Najeriya
- Ba da yawunmu wani tsagin tsohuwar CPC ya goyi bayan Tinubu ba – Malami
Ayuba Wabba yace ma’aikata da sauran yan Najeriya sun shiga damuwa kan yadda gwamnati ta yanke shawarar kara kudin man fetur da na wuta, a daidai lokacin da sauran kasashe a fadin duniya ke kokarin saukawawa mutanensu wahalhalun rayuwa domin rage illar annobar corona.
A cewar Ayuba Wabba, kwamitin aikin kungiyar na kasa ya gano cewa annobar corona da matsin tattalin arzikin da kasa ke ciki ya jawowa yan Najeriya wahalhalu da dama, kuma a yanzu karin farashin ya sake tagayyara su.