Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen tsawa da rana a wasu sassan fadin kasar nan.
Sanarwar NiMet da aka fitar a jiya Alhamis a Abuja ya yi hasashen yanayin rana a yankin arewa a ranar Juma’a.
Hukumar ta sa ran za a samu karancin tsawa a sassan jihohin Kebbi, Zamfara da Kaduna a lokutan rana da kuma yamma.
Hukumar ta ce ana sa ran samun yanayin rana tare da gajimare a yankin Arewa ta Tsakiya da safe. Hukumar ta yi hasashen za a yi tsawa a wasu sassan jihohin Kebbi, Zamfara, Taraba da Kaduna da yammacin ranar.