Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, ya ce Nijeriya na bukatar zuba jarin kusan dala tiriliyan 3 nan da shekaru 30 masu zuwa domin dakile taɓarɓarewar ababen more rayuwa a kasar.
Abbas ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da aikin gina titin Ring Road zuwa kwatas din alkalai a babban birnin tarayya, Abuja.
Hon. Benjamin Kalu, Wanda ya wakilci mataimakin kakakin majalisar, ya yi nuni da cewa, samar da ababen more rayuwa ba wai ginshikin tattalin arziki ba ne kawai, a’a shi ne ginshikin ci gaban kasa. Tun da farko, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Barista Nyesom Wike, ya gode wa Shugaban Majalisar da Majalisar Dokoki ta kasa bisa goyon bayan da suka ba shi, ya kuma bukaci dan kwangilar da ya kammala aikin a cikin lokaci, wanda zai bai wa Shugaban kasa Bola Tinubu damar kaddamar aikin a yayin da yake bikin cika shekaru biyun a shugabancin kasar.