Nijeriya ba ta cikin jerin ƙasashen da suka fi dogaro da lamuni daga IMF a Afirka

0 33

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya fitar da rahoton jerin ƙasashen 10 da suka fi cin bashi a nahiyar Afirka, a lokacin da ƙasashen ke fama da matsanancin bashin da ya dabaibaye su.

Rahoton ya bayyana cewa, duk da ɗimbin bashin da Nijeriya ke karɓowa, ba ta cikin jerin ƙasashen da suka fi dogaro da lamuni daga IMF a Afirka.

Akwai ƙasashe 10 da suka yi fice wajen karɓar bashin IMF, galibi don cike gibin kasafin kuɗi da kuma magance matsalolin tattalin arziƙi.

Koyaushe, IMF na gindaya tsauraran sharuɗa, kamar cire tallafi, rage darajar kuɗaɗen ƙasa, da tsuke bakin aljihu kafin bayar da bashin. Dogaron ƙasashen Afirka kan bashin IMF yana nuna karuwar matsalolin tattalin arziƙi, yayin da suke ƙoƙarin cike gibin kasafin kuɗi da cimma burin ci gaba mai ɗorewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: