NEMA: Mutane miliyan 2 da dubu 353 da 647 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a bara.

0 184

Darakta-Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Muhammadu Muhammed, ya ce mutane miliyan 2 da dubu 353 da 647 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a bara.

Ya fadi haka ne jiya a Abuja yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na hukumar na shekarar 2020 ga Ministar Jin Kai, Kula da Annoba da Walwalar Jama’a, Sadiya Umar Farouq.

Ya ce daidai lokacin da ake fama da rikice-rikice a duniya, Najeriya ba ta tsira daga wasu munanan abubuwan da suka faru, wadanda suka hada da ambaliyar ruwa, gobara, tayar da kayar baya, fashi da makami, satar mutane, hatsarin mota, fashewar bututun mai and iskar gas, rikicin makiyaya da manoma, rikicin kabilanci, satar shanu, rushewar gine-gine wanda duk sun haifar da raba mutane da gidajensu a fadin kasarnan.

Yace hukumar NEMA na kaddamar da na’urorin rage aukuwar hatsari don bincike da ceto mutane a fadin kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: