NDLEA ta damke wasu mutane 363 da take zargi da safarar miyagun kwayoyi a Jigawa

0 248

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Jigawa NDLEA ta damke wasu mutane 363 da take zargi da safarar miyagun kwayoyi da dillancinta a jihar daga watan Yunin 202 zuwa yanzu.

Kwamandan hukumar ta jihar Hajiya Maryam Gambo ta sanar da haka a ranar Asabat ranar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya, wanda aka gudanar a helkwatar hukumar dake Dutse.

Hajiya Maryam ta bayyana cewa cikin adadin 147 maza ne yayin da sauran mata ne.

Ta kara da cewa ankai wadanda ake zargi 108 kotu kuma an same su da laifi.

Maryam ta kara da tace an same su da killograms 344. 9 Marijuana an kuma karbe su da sauran kayan maye a jihar

Kwamndan ta ci gaba da cewa jumilar wadanda ake zargi 300an gurfanar dasu a gaban koto.

Leave a Reply

%d bloggers like this: