Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta ce nan ba da jimawa ba za ta gabatar da hujjoji na cin zarafi ta hanyar lalata da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi mata.
“A lokacin da ya dace kuma a wurin da ya dace, zan gabatar da hujjojin da nake da su,” in ji sanatar a shirin Politics Today na gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis.
Ta kuma ce, ko da yake matakin Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) na kin karɓar takardar koke na neman yi mata kiranye daga kujerarta ya zo da a kurace, amma ya yi daidai.
“Ina lauya. Ina sanata kuma na fahimci yadda Najeriya ke tafiya. Abu mafi muhimmanci a gare ni shi ne cewa an dakatar da wannan yunƙurin tunbuke ni daga majalisa.
“Ina yabawa INEC duk da cewa na yi imani ya kamata su yi watsi da wannan koke tun farko,” in ji ta.
Jigo a jam’iyyar PDP ta ce yawancin adireshin da aka bayar a cikin takardar neman tunbuke ta daga majalisa ba su inganta ba, domin mafi yawan gidaje a yankinta ba su da alamomin adireshi.