Nakasu ne mallakar kwalin Degree ba tare da wata kwarewa a sana’ar hannu ba – Farfesa Ishaq

0 275

Farfesa Ishaq Oloyede dake zama magatakardar hakumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB, ya bayyana takardar shaidar kammala degree ba tare da wata kwarewa a sana’ar hannu a matsayin nakasu.

Ishaq Oloyede  ya bayyana haka ne yayin bakin yaye dalibai karo na 10 da 11 a jami’ar jihar Kwara dake Malete.

Yace kammala jami’a baya nufin daina daukar darasi, face wani mafari ne a jami’ar rayuwa. Ya kara da cewa ya kamata dukkan dalibai su shiryawa kalubalen rayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: