Najeriya ta samu dala biliyan 34 da miliyan 220 daga bangaren mai da iskar gas a shekarar 2019

0 225

Hukumar dake binciken yadda ake kashe kudaden da ake samu daga ma’​adanan man fetur a kasarnan a rahoton bayananta na baya-bayanan ta bayyana cewa Najeriya ta samu dala biliyan 34 da miliyan 220 daga bangaren mai da iskar gas a shekarar 2019.

Rahoton ya nuna yadda kudaden shigar da aka samu ya karu da kashi 4.88 akan dala biliyan 32 da miliyan 630 a shekarar 2018.

Rahoton na shekarar 2019 ya shafe masana’antu 98 ciki har da kamfanoni 88 na mai da iskar gas, da hukumomin 9 da kamfanin iskar gas na kasa NLNG.

Kiddigar kudaden shigar da aka samu ya nuna kamfanoni sun biya kudaden da suka kai dala biliyan 18 da miliyan 900, yayin da kudaden da gwamnati ta samu ta sayar da mai da iskar gas ya kai dala biliyan 15 da miliyan 320.

Cikkaken bayanin rahoton ya nuna cewa cikin shekaru 10 daga 2010 zuwa 2019, yawan kudaden da gwamnati ta samu daga mai da iskar gas ya kai dala biliyan 418 da miliyan 540, inda aka fi samu kudade a shekarar 2011 bayan an samu dala biliyan 68 da miliyan 440, yayin da shekarar da aka samu mafi karancin kudade ita ce 2016, inda aka samu dala biliyan 17.

Leave a Reply

%d bloggers like this: