Najeriya ta sake kiran da a sako Bazoum da matarsa

0 110

A ranar Juma’a ne Najeriya ta sake kiran da a sako hamɓararren shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum da matarsa.

Mohammed Bazoum ya kasance a tsare tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki a ƙasar a watan Yulin 2023.

An hamɓarar da gwamnatin nasa ne a ranar 26 ga watan Yulin 2023, bayan ya shafe shekaru a kan mulki.

Shugaban masu tsaron lafiyarsa Janar Abdourahamane Tiani, ne ya jagoranci hamɓarar da gwamnatin Bazoum ɗin bayan zarge-zargen gaza kare ƙasar daga hare-haren masu iƙirarin jihadi.

Tun daga lokacin ne Bazoum da mai ɗakinsa Hadiza ke tsare a fadar gwamnatin ƙasar da ke Yamai.

A don haka ne gwamnnatin Najeriya ta bakin ministan yaɗa labaran ƙasar Mohammed Idris, ya yi kiran ta kafar yaɗa labaran Faransa TV Network France 24 kan a sako Bazoum da mai ɗakinsa.

Ministan ya ce,”Muna so a fito da shi. Muna ganin bai aikata wani laifi ba, shi ɗan siyasa ne, a don haka idan kuna son cire shi sai ku bi tsarin yadda dimokuraɗiyya ta tanada.”

Ƙungiyoyi da ƙasashe da dama ciki har da ECOWAS da Majalisar Ɗinkin Duniya ne sun sha yin kira kan a sako Bazoum.

Leave a Reply