Najeriya Ta Rasa Sojoji Da ‘Yan Sanda 965 A Cikin Shekaru Biyu

0 142

Akalla sojoji da ‘yan sanda 965 ne suka mutu a bakin aiki, sakamakon karuwar tashe-tashen hankula a sassan Najeriya da dama, a yaki da kungiyoyin  Boko Haram, da ‘yan bindiga, da sauran masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa tashe-tashen hankula daban-daban da suka shafi kashe jami’an ‘yan sanda da sojoji tsakanin watan Janairun 2021 zuwa Afrilu 2023, inda sakamakon binciken ya nuna cewa jami’an tsaron Najeriya na fama da kashe-kashe da wasu mutane da ba na gwamnati ba.

bayanan, wanda aka tattara na musamman daga abubuwan da suka faru a jaridu, sun nuna cewa ‘yan sanda 581 da jami’an soji 384 ne suka mutu a bakin aiki a cikin wa’adin.

Sai dai manyan hafsoshin da suka yi ritaya, sun ce lamarin, ko da yake abin takaici ne ba zai yi tasiri ga kwarjinin jami’an tsaron ba. Sai dai bayanai sun nuna cewa hukumar ta yan sanda tana da kusan jami’ai dubu 371 da 800 a fadin kasar, inda adadin ya nuna duk dan sanda daya na kare rayukan yan kasa 540. Wannan ya yi kasa da adadin shawarar da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar na alhakin mutane 450 akan kowane dan sanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: