Najeriya ta kuduri aniyar kawar da cutar shan inna – Kashim Shettima

0 312

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce Najeriya ta kuduri aniyar kawar da cutar shan inna nan da karshen wannan shekara.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da daya daga cikin attajiran duniya, Bill Gates, ya nanata kudurin gidauniyarsa na baiwa Afirka dala biliyan 7 nan da shekaru hudu masu zuwa.

Har ila yau, hamshakin dan kasuwan Afrika, Aliko Dangote yace daukar mataki na musamman daga shugabannin kasar nan ne kawai zai tabbatar da cimma muradun ci gaba mai dorewa.

Sun yi wannan jawabi ne a jiya yayin wani taro da ya samu halartar wasu gwamnoni karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya a dakin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban kasa a Abuja.

Idan zamu iya tunawa dai gidauniyar Bill & Melinda Gates a watan Nuwamba 2022 ta ce zata bayar da dala biliyan 7 ga Najeriya da sauran kasashen Afirka a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Gidauniyar ta ce alkawarin kudin da sukayi ya kai kaso 40 cikin 100 na kudaden da aka kashe a cikin shekaru hudun da suka gabata. Kudin kuwa da za’a kashe nan gaba za’ayi amfani da su domin magance yunwa, cututtuka, fatara da kuma rashin daidaito tsakanin jinsi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: