Sabbin bayanai daga Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) sun nuna cewa Najeriya ta kashe sama da naira biliyan 520 wajen shigo da makamai a shekarar 2024.
Rahoton ya nuna cewa tsakanin 2020 zuwa 2024, an kashe jimillar naira biliyan 777.1 wajen shigo da makamai daga ƙasashen waje.
Wannan ya zo ne duk da ikirarin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, cewa Najeriya ta fara fitar da makamai zuwa wasu ƙasashen Afirka.
Duk da wannan ikirari, bayanai sun nuna cewa Najeriya ta fitar da makamai a 2021 kawai, inda darajar fitar da su ta kai naira miliyan 192.64, ba tare da bayyana ƙasashen da aka fitar musu da su ba.