Najeriya Da Andulus Zasu Ƙulla Alaƙa

0 409

Kasar Spaniya za ta kulla alakar kasuwanci da Najeriya da nufin habaka harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Jakadan kasar Spaniya a Najeriya Mr. Marcelino Ansorena ya bayyana hakan yayi da yake ganawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce Spaniya ta zabi kulla alakar kasuwanci da Najeriya daga cikin kasashen Afrika sakamakon harkokin saye da sayarwa dake wanzuwa tsakanin kasashen hadin kan ECOWAS.

Kazalika jakadan ya bayyana cewa gwamnatin kasar Spaniya ta kudiri aniyar karfafa harkokin kasuwanci tsakaninta da gwamnatin Najeriya nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: