NAHCON Ta Bada Wa’adin Zuwa Gobe Juma’a A Matsayin Ranar Karshe Ta Kammala Biyan Kudaden Aikin Hajjin Bana
Hukumar alhazai ta kasa ta bada wa’adin zuwa gobe Juma’a a matsayin ranar karshe ta kammala biyan kudaden aikin hajjin bana daga hukumomin kula da jin dadin Alhazai na jihohi.
Shugaban Hukumar Zikrullah Kunle-Hassan ne ya bayar da wannan umarni a jiya a wajen wani gagarumin taron da shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na jihohi a gidan Hajji da ke Abuja.
A cewar wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda-Usara ta fitar, an kira taron ne domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi kudaden da maniyyata ke biya na aikin hajji domin kammala samun adadin wadanda suka cancanci zuwa aikin hajjin bana daga Najeriya.
Sanarwar ta yi nuni da cewa, tantance adadin zai tabbatar da alkaluman da za a kulla yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama.
A wani labarin kuma, Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga na Hukumar, Suleman Momoh, ya bayyana cewa za a gudanar da tantance rukunin farko na likitocin aikin Hajji na bana a yau, inda ya kara da cewa za a gudanar da taron wayar da kan jama’a da sauran taruka bayan tabbatar da wadanda suka yi nasara.