Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC ta nemi hukuncin kisa ga masu haɗawa da shigar da jabun magunguna.
A cewar shugabar hukumar Mojisola Adeyeye, tsauraran matakai ne kawai za su hana aikata hakan musamman idan lamarin na kai wa ga mutuwar yara.
”Wani ya sayi magani naira 13,000 a wani kanti, wani kuma ya sayi irin wannan maganin a wani shagon kan naira 3,000, hakan ya ankarar da mu, kun san mene ne? da muka gwada maganin a ɗakin gwaje-gwajenmu da ke Kaduna, babu wani sinadarin magani mai amfani a cikin shi, a don haka ina son a fara aiwatar da hukuncin kisa,” in ji ta a wani hira da gidan talibijin na Channels.
Ko a jiya ma majalisar wakilai ta buƙaci babban mai shari’a na tarayya da ya gabatar da tsauraran takunkumai da suka hada da ɗaurin rai da rai ga masu haɗawa da masu shigo da magungunan jabu cikin ƙasar.
Bayan muhawara kan ƙudurin wanda ya samu goyon bayan ƴan majalisar, majalisar ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyara ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri.
– BBC Hausa