Na yi almajiranci kafin na zama shugaban NNPCL – Mele Kyari

0 54

Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, Mele Kyari ya ce yana godiya ga Allah da ɗaga darajarsa daga wanda ya taɓa karatu a makarantar tsangaya ta amajirai har ya kai ga zama shugaban NNPCL a Najeriya.

Mele Kyari ya bayyana haka ne a shafinsa na X, a saƙonsa na godiya ga Allah bisa cika shekara 60 a duniya.

A cewarsa, “cikin ikon Allah, a yau nake cika shekara 60 a duniya, duk da na riga na kai tun a baya idan aka yi la’akari da watan musulunci. Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar zama shugaban kamfanin makamashi mafi girma a Afirka.”

Kyari ya ce yana godiya ga tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ma Najeriya bisa wannan damar da ya samu.

“Idan na waiwayi baya, nakan tuna gwagwarmayar da na sha. Nasarori da ƙalubale waɗanda Allah ne kaɗai ya san yadda na samu nasarar kai wa ga matakin da nake ciki yanzu.”

Ya ce yanzu ya ƙara samun ƙarfin gwiwar hidimta wa ƙasarsa, sannan ya yi godiya da malamansa na tsangaya da na boko da sauran ƴan uwa da abokan arziki, tare da neman yafiya ga duk waɗanda ya saɓa musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: