Na gaji da cigaba da zama gwamnan Zamfara – Matawalle

0 191

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, yace ya gaji da cigaba da zama gwamnan jihar saboda yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane daga ‘yan ta’adda.

Bello Matawalle ya sanar da haka yayin da aka zanta da shi a gidan rediyon DW Hausa, lokacin da yake mayar da martani akan faduwarsa zabe.

Gidan rediyon Sawaba ya bayar da labarin cewa Bello Matawalle, wanda ya nemi zarcewa a karkashin jam’iyyar APC, ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Dauda Lawal.

Amma da yake mayar da martani akan rashin nasararsa, Bello Matawalle yace burinsa ya cika bayan mulkar jihar na tsawon shekaru hudu.

Bello Matawalle, wanda yayi zargin cewa hukumar soji ta turo da motoci 300 na sojoji zuwa jihar, yace ya samu bayanin dake cewa an shirya daukar mataki akansa da sauran gwamnonin da suka soki matakin sake fasalin Najeriya na gwamnatin tarayya. Ya kuma ce hurumin daukar mataki akan sakamakon zaben na jam’iyyarsa ne ba nasa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: