Mutum daya ya rasu, 14 sun jikkata a sakamakon ambaliyar ruwa a Damaturu

0 336

Daruruwan iyalai sun shiga cikin halin kaka-ni-ka yi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe sakamakon aukuwar ambaliyar ruwa a ranar Laraba data gabata.

Yanzu haka suna rarrabe ne a gidajen ‘yan uwa da abokan arziki, da makarantu da gidajen mai, bayan ambaliyar ruwa ta raba su da muhallansu.

Sai dai ana sa ran za a kai masu dauki a yau Asabar, bayan da gwamnatin jihar ta tantance ire-iren tallafin da suke bukata.

Ambaliyar ruwan, wadda ta shafi wasu unguwanni a garin na Damaturu, babban birnin jihar Yoben, ta jefa jama’a da dama cikin tsaka mai wuya.

Hakumar bayar agajin gaggawa ta jihar tace mutum 1 ya rasa rayuwarsa yayin da wasu 14 suka samu munanan raunuka.

Babban sakataren hakumar Muhammad Goje yace bincikensu ya tabbatar da cewa lamarin ya shafi gidaje 200 a yakin Ganyen Kura, da wasu 3 a Malari, sauran yankunan sun hada da kan hanyar Gujba, Pompomari, Nayi-Nawa, da Bulabulin. Yayin da yake jajanta musu, yace hakumar agajin zata tallafa musu a matakin farko.

Leave a Reply

%d bloggers like this: