Mutum 7 sun mutu yayin zanga-zangar bayan zaɓe a Mozambique

0 176

Aƙalla mutum bakwai ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a zanga-zangar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar ranar 13 ga watan Nuwamba a lardin Nampula da ke arewacin ƙasar Mozambique.

Wata ƙungiyar kare hakkin fararen hula ta bayyana cewa zuwa yanzu alkaluman waɗanda suka mutu a rikicin da ya fara tun 21 ga watan Okotoba, ya kai aƙalla mutum 47.

Ƙungiyar ta ce ƴansanda sun harbe masu zanga-zanga a lardin Namicopo da ke birnin Nampula mai yawan jama’a.

Rahotanni sun ce kashe mutanen ya sa mazauna Namicopo fara farautar ƴansandan da ake zargi da aikata kisan.

Lamarin ya kai ga jikkata wani jami’in ɗan sanda ɗaya.

Dubban mutane ne suka fita kan titunan birane da kuma garuruwa don yin Alla-wadai da zargin tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 9 ga watan Oktoba.

  • BBC Hausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: