Wani hatsarin jirgin ƙasa a Mexico ya yi sanadin mutuwar mutum 20 tare da jikkata wasu da dama ranar Litinin a babban birnin ƙasar.
An ga yadda taragon jirgin ke reto a jikin wata gada cikin wasu wayoyi, inda goshin jirgin ke kallon ƙasa.
“Abin baƙin ciki mutum 20 ne suka mutu zuwa yanzu, ciki har da yara,” a cewar Magajin Garin Mexico City, Claudia Sheinbaum.
Sashen tsaro na birnin ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa kusan mutum 70 ne suka ji raunuka.