Mutum 2 ne suka mutu yayinda kuma aka sace wasu mutum 20 a wani hari da yan bindiga suka kai jihar Kaduna
Kimanin mutane 2 ne suka mutu, yayinda kuma aka sace mutane 20 a wani hari da yan bindiga suka kai Unguwar Gimbiya dake karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Da yake tabbatar da gaskiyar lamarin ga gidan Talabijin na Channels Tv, Kakakin Rundunar Yan sandan Jihar Kaduna ASP Muhammed Jalige, ya ce yan bindigar sunje garin ne da misalin karfe 1 na Dare.
Haka kuma ya ce bayan zuwan su garin ne yan bindigar suka budewa Mutane wuta a lokacin da suke barchi, wanda hakan ne ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu.
Kakakin yan sandan ya ce yan bindigar sun kuma sace mutane 20 wanda sune zaune a garin kafin zuwa Jami’an tsaro.
Kazalika, ya ce gamayyar Jami’an tsaro sun kaddamar da wani shiri domin bibiyar wadanda sukayi Garkuwa dasu din.