A kalla Matasa Maza da Mata dubu 1,466 ne ake saran tantancewa bayan sun samu Damar shiga Shirin gwamnatin tarayya na Npower a nan karamar hukumar Hadejia.
Shugaban Kula da Shirin Tallafi na Karamar Hukumar Hadejia Alhaji Isah Idris Abubakar, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban Karamar hukumar wanda ya kai ziyara domin ganewa idanun sa kan yadda aikin tantancewa yake wakana.
A cewarsa, Ma’aikatar Jinkai, Iftila’i da Cigaban Al’umma ce ta kirkiri shirin Saturday 10th SAFFAR 1443, 18th September 2021da nufin dakile fatara da talauci a tsakanin Matasa.
Malam Isah Idris Abubakar, ya ce za’a shafe kimanin Makonni 3 ana tantance Matasan domin tabbatar da cewa babu wanda aka bari a baya.
Haka kuma ya bukaci wadanda aka zaba din su kasance masu yin hakuri kasancewar shirin babu wanda zai bari a baya har sai an tantance shi.
A jawabinsa, Shugaban Karamar Hukumar Hon Abdulkadir Bala Umar T.O ya yabawa Ma’aikatar Jinkai, Iftila’i da Cigaban Al’umma bisa kirkirar shirin, inda ya ce zai taimakawa matuka wajen ragewa Matasa radadi.
Kazalika, ya shawarci Matasan su kasance masu yin amfani da damar da aka basu wajen yin abinda ya kamata.