Mutum 11 ne suka tsere daga wata Maboyar da wasu yan Bindiga da suka sace su a jihar Kaduna

0 154

A kalla Mutane 11 ne suka tsere daga wata Maboyar da wasu yan Bindiga da suka sace su a garin Sabon Birni na karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa bayan tantancewa sun gano cewa mutanen an sace su ne daga kyauyen Dumbin Rauga na karamar hukumar Zaria wanda yake kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Daga cikin su akwai wadanda basu wuce shekaru 7 zuwa 10 ba, kuma dukkanin su sun fito ne daga kyauyen Dumbin Rauga na garin Zaria.

Shida kuma daga cikin su Fasinjoji ne da suke tafiya birnin Ilorin na Jihar Kwara bayan sun taso daga Birnin Maiduguri na Jihar Borno, inda aka sace su a hanyar Zaria zuwa Kaduna.

Kawo yanzu, Jami’an tsaro sun mika mutanen 11 ga Yan Uwansu.

Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da gaskiyar Labarin ga gidan Talabijin na Channels Tv.

Leave a Reply

%d bloggers like this: