Mutane uku sun mutu jim kadan bayan kammala zaben shugaban kasar Mauritaniya

0 150

Akalla mutane uku ne aka ruwaito sun mutu jim kadan bayan kammala zaben shugaban kasa a Mauritaniya, sakamakon arangamar da aka yi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.

An yi zanga-zangar a babban birnin kasar da ma wasu sassan kasar a daren ranar Litinin bayan sanar da shugaba Mohamed Ould Ghazouani a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sai dai, Biram Dah Abeid, dan takarar da ya zo na biyu kuma fitaccen mai fafutukar yaki da bauta, ya zargi hukumomi da zamba ya kuma yi ikirarin cewa an tafka magudi a sakamakon zaben. Hukumomin kasar sun sanar da cewa jami’an tsaro sun yi arangama da masu zanga-zanga a birnin Kaedi, birni mafi girma a yankin kudancin kasar, kuma tungar ‘yan adawa da ke da dimbin bakaken fata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: