Mutane na cigaba da rasa rayukansu sakamakon nau’in cutar korona ta Omicron a Birtaniya
Aƙalla mutum ɗaya ya rasu sakamakon nau’in cutar korona na Omicron a Birtaniya, a cewar Firaminista Boris Johnson.
Shugaban ya ce nau’in cutar ya kuma haddasa kwantar da mutane a asibiti, yana mai cewa “abu mafi muhimmanci” da mutane ya kamata su yi shine su je a jaddada musu rigakafi.
Da yakai ziyara wani asibiti a Landan, Boris Johnson ya ce ya kamata mutane su daina tunanin cewa Omicron ƙaramin nau’i ne.
Firamistan ya ce abin takaici, da gaske Omciron na haddasa jinya a asibitoci kuma har mutum ɗaya ya mutu.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce bayyana fargaba kan yaduwar cutar, inda ta gargadi shugabannin Duniya su dauki matakan dakile yaduwar ta.