Hakumar lura da shaidar dan kasa tace kimanin mutane miliyan 117 ne zuwa yanzu suka yi rajistar mallakar katin shaidar zama dan kasa da lambar NIN.
A cewar sabbin alkaluman da hakumar ta fitar daga shafin ta mutane miliyan 66.281 da suka yi registar sun kasance maza, wanda ke zama kashi 56.6 yayin da kashi 43.5 wanda yawansa ya kai miliyan 51.079 suka kasance mata.
Haka kuma bayanan sun nuna cewa jihar Legas ita ce kan gaba a yawan wadanda suka yi registar da mutane miliyan 12,6, sai jihar Kano dake biye da ita a mataki na biyu da yawan mutane miliyan 10.2.
Jihohin bayelsa, Ebonyi da Ekiti ne jihohin da suke kasa a yawan mutanen suka yi rejista da lambar shaidar zama dan kasar.