Mutane huɗu sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar kwalara ce a Jihar Adamawa

0 138

Wani rahoto na cewa mutane huɗu sun mutu sakamakon wani lamari da ake zargin ya kasance ɓarkewar cutar kwalara ce a karamar hukumar Yola ta Arewa, Jihar Adamawa.

Shugaban ƙaramar hukumar, Barista Jibril Ibrahim, ya tabbatar da ɓarkewar cutar a yankunan da lamarin ya shafa, ciki har da Alkawa, da Ajiya, da Limawa. 

Ya bayyana cewa akwai mutane 40 suna karɓar magani a Asibitin kwararru na Yola, inda gwaje-gwajen lafiya suka tabbatar da kasancewar cutar cholerae.

Ma’aikatan lafiya suna sa ido sosai kan halin da ake ciki, suna ziyartar gidaje domin wayar da kan jama’a da hana yaɗuwar cutar. 

A nasa ɓangaren, kwamishinan lafiya na jihar, Mista Felix Tangwami, ya bayyana cewa suna jiran sakamakon ƙarshe daga dakin gwaje-gwaje, kuma ya ce wasu daga cikin waɗanda suka mutu ba su kai ga zuwa cibiyoyin lafiya ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: